Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake jaddada cewa za a cigaba da amfani tsofaffin takardun Naira. Bankin ya mayar da martani a daren Juma’a bayan samun jita-jitar da ke cewa tsofaffin takardun za su daina zama halattacciyar hanyar biyan kudi a karshen wannan shekara. Amma babban bankin, ta bakin mukaddashin daraktan sadarwarsa, Misis Hakama Sidi
Har yanzu ana amfani da tsofaffin takardun Naira – CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake jaddada cewa za a cigaba da amfani tsofaffin takardun Naira.
Bankin ya mayar da martani a daren Juma’a bayan samun jita-jitar da ke cewa tsofaffin takardun za su daina zama halattacciyar hanyar biyan kudi a karshen wannan shekara.
Amma babban bankin, ta bakin mukaddashin daraktan sadarwarsa, Misis Hakama Sidi Ali, ta karyata kirari a matsayin mara tushe.
“Babban Bankin Najeriya ya samu labaran karya da ake yadawa dangane da ingancin tsofaffin takardun kuɗi na ₦1000, ₦500, da ₦200 da ke yawo a halin yanzu.
“CBN na sake jaddada cewa hukuncin kotun koli da aka yanke a ranar 29 ga Nuwamba, 2023, ya bai wa tsofaffi da sabbin nau’ukan takardun ₦1000, ₦500, da ₦200 damar yawo tare ba tare da wani wa’adin daina amfani da su ba.
“Domin kawar da duk wani rashin fahimta, dukkan nau’ukan takardun Naira, ciki har da tsofaffi da sabbin nau’ukan takardun ₦1000, ₦500, da ₦200, ₦100, suna nan da inganci kuma za a ci gaba da amfani da su a matsayin halattacciyar hanyar biyan kuɗi ba a tare da sanya wa’adi ba.”
Har yanzu ana amfani da tsofaffin takardun Naira – CBN
Like this:
Like Loading...